Categories
Siyasa

‘Yan sandan Kano sun hada kai da gwamnati domin cutar da mu – NNPP

Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP

Rabi'u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar NNPP

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta zargi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda da hada kai da gwamnatin jihar ta APC domin kawo mata nakasu a zabe mai zuwa.

A wani taron manema labarai da ta kira, Jam’iyyar ta NNPP ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya kame mambobinta sama da 100 ba tare da wani dalili ba, inda ta yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan kasar ya cire kwamishinan jihar.

Dr Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi ne dan takarar Sanata na jam’iyyar, ya shaida wa manema labaran cewar sun bada tsawo sa’o’i 24 a saki mambobinsu ko su tsunduma zanga-zangar lumana.

Wakilin RFI Hausa, Abubakar Abdulkadir Dangambo ya yi kokarin jin ta bakin ‘yan sandan na Kano kan wannan zargi, sai dai har zuwa yanzu kakakin rundunar bai amsa kiran da manema labarai suka yi masa ba.

Kazalika, ita ma gwamnatin Kano ba ta ce komai tukunna game da zargin.

Categories
Siyasa

A rana mai kamar irin ta yau ne a kashe tsohon shugaban Najeriya-Murtala Ramat

A rana mai Kamar Ta Yau 13 ga Fabrairun 1976, A ka kashe Shugaba mulkin Soja Na Tarayya Najeriya General Murtala Ramat Muhammad a Wani yunkurin juyin mulki.

An kuma kashe direbansa Da Gwamnan Mulkin Soja Na jihar kwara Kanal Ibrahim Taiwo.

Yunkurin juyin mulkin Nijeriya a shekarar 1976 wani yunkuri ne na juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijeriya ranar 13 ga Fabrairun 1976 a lokacin da wani bangare na hafsoshin Sojin kasar karkashin jagorancin Laftanar Kanar Bukar Suwa Dimka suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Janar Murtala Mohammad. (wanda ya karbi mulki a juyin mulkin 1975 ).

An kashe Janar Murtala Muhammad a Legas tare da mataimakinsa Laftanar Akintunde Akinsehinwa a lokacin da wasu sojoji karkashin Dimka suka yi wa motarsa ​​kwanton bauna a Ikoyi kan hanyar zuwa Barrack Dodan. A cikin shirye-shiryen Rediyo Da Aka watsa ga al’ummar kasar, Dimka ya ambaci cin hanci da rashawa, yanke hukunci, kamawa da tsarewa ba tare da shari’a ba, Da rauni daga bangaren Gwamnatin Murtala da rashin iya gudanar da mulki a matsayin dalilan kifar da gwamnati.

Sojojin gwamnati Masu Biyayya Ga Gwamnati sun murkushe yunkurin juyin mulkin bayan sa’o’i da dama.

Bayan farautar makwanni uku, Ana Neman Dimka Daga Bisani an kama Dimka a kusa da Abakaliki a kudu maso gabashin Najeriya a ranar 6 ga Maris 1976.

Laftanar Janar Olusegun Obasanjo ne ya gaji Janar Murtala Muhammad a matsayin shugaban kasa.

A lokacin da mulkin Obasanjo tare da makaranban shi a Gwamnati, da suka hada da  shehu Musa Yar’adua da TY Danjuma da IBB da Domkat Bali sun yi kokarin ganin sun aiwatar da ayyukuna da Murtala ya kudurta gudanarwa a Najeriya.

Saboda kimar Janar Murtala Muhammad ne a Najeriya, aka saka hotonsa cikin kakin Soji a kudin kasar Naira Ashirin.

Categories
Siyasa

Shugaba Buhari na shirin tafiya a kasar Senegal

Buhari

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai tafi ƙasar Senegal ranar Talata domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.

Taron wanda shugaban Senegal kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, Macky Salla zai karɓi baƙunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.

Mista Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu ƙasashen, ciki har da Najeriya.

Ya ƙara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin ƙagin yunwa, taron – wanda shugabannin ƙasashen Afirka da ministocin kuɗaɗen da na noma na nahiyar, da ƙungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.

Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.

Article share tools

Categories
Labaran Duniya Nishadi Rahoto Siyasa Wasanni

Mutane 15 doka tasa halewa ayi musu jiniya a Najeriya -Abba Hikima

Duk Nigeria mutane 15 doka ta sahalewa yin amfani da jiniya. A ciki babu shugaban jami’an tsaro na farin kaya ballantana matar sa. Kuma hukuncin yin amfani da jiniya ga wanda doka bata sahalewa ba zaman gidan yari ne na wata 6.

Barin mutanen da basu cancanci a musu jiniya ba yin amfani da ita yana kara kumbura musu kai. Yana sa su girman kai da raina mutane. Kuma ya jawo raina doka.

Saboda haka, ya kamata yan sanda su kama wannan mata su gurfanar da ita a gaban kotu a bisa wannan laifi da sauran laifuffukan da suka fito fili.

Kuma indai shugabanni; zababbu da nadaddu basu takawa matan su da iyalan su birki akan shiga harkokin mulki ko bawa jami’an Nigeria umarni ba, to zaune bata kare mana ba a wannan kasa. Dan na tabbata wata rana wata shafaffiya-da-man in taci ta koshi, cewa za tayi a kamo mata shugaban sojoji.

Categories
Labaran Duniya

Sabuwar Gwamnati mai zuwa a Najeriya zata Gaji tiriliyan 77

Shugabar Ofishin Kula da Basuka a Najeriya Patience Oniha ta ce duk gwamnatin da za ta gaji ta Shugaba Muhammadu Buhari a ƙarshen watan Mayu za ta tarar da bashin da ya kai kusan naira tiriliyan 77.

Ta bayyana haka ne ranar Laraba yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da kasafin kuɗin ƙasar na 2023, wanda gwamnatin za ta cike giɓinsa ta hanyar ciyo bashi.

Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta ce za a samu kashi 22 cikin 100 na kuɗin shigar da aka yi hasashe ta hanyar cinikin man fetur, yayin da za a samu kashi 77 daga wasu harkokin daban.

Don cike giɓin, ministar ta ce sai an karɓo bashin naira tiriliyan 7.04 a cikin ƙasar da kuma tiriliyan 1.76 daga ƙasashen waje. Haka nan za a karɓo tiriliyan 1.77 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma sayar da kadarorin gwamnati da za su samar da naira biliyan 206.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan kasafin kuɗin na 2023 kan sama da naira tiriliyan 20, wanda ke da giɓin tiriliyan 11.

Categories
Labaran Duniya

Trump ya ƙaryata rahotan bayanan takardu biyan Harinji sa

Wani kwamitin majalisar dokokin Amurka ya fitar da bayanan haraji na tsohon shugaba Donald Trump na tsawon shekara shida.

Tsohon shugaban ya kwashe shekaru yana kokarin boye takardun – amma a watan jiya kotun kolin ta amince a bayyana su Bayanan harajin da kwamitin da yan jam’iyyar Democrat suka jagoranta sun nuna a cikin shekara guda, Mista Trump ya biya dala dari bakwai da hamsin kacal na haraji na gwamnatin tarayya, a wani lokacin kuma ba ya biyan komi.

Donald Trump ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa babu cikakkun bayanan da kowa zai iya fahimta. tare da sukar yan majalisar Democrat wadanda ya kira abin kunya ga majalisar Amurka

Categories
Siyasa

Gwamnatin tarayy Najeriya tace zata ƙarawa Ma aikata Albashi Ministan Gwadago-Ngige

Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ƙasar.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Villa.

Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.

Da aka tambaye shi sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ”ƙwarai kuwa, wannan shi ne abin da nake faɗa cewa kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata ta ƙasar”.

“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin”, in ji ministan.

Kan batun albashin wata takwas da malaman jami’o’in ƙasar ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.

Article share tools

Categories
Labaran Duniya

A ƙalla mutum 20 suka Mutu sakamakon Haɗarin mota

Akalla mutum 20 ne suka mutu a wasu haɗuran mota biyu da suka auku a wurare biyu a Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta ƙasar Bisi Kazeem ya sanya wa hannu ya ce daya daga cikin haɗuran biyu ya auku ne a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yayin da ɗayan kuma ya auku a hanyar Mokwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutum 10 ne suka mutu a haɗarin hanyar Ibadan yayin da shida suka jikkata.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa wasu mutum 10 sun mutu a haɗarin da ya auku a hanyar Mokwa, tara nan take ɗaya kuma bayan an kai shi asibiti.

Sanarwar ta ambato muƙaddashin shugaban hukumar Dauda Biu na kokawa game da saɓa wa dokokin gudun wuce kima da mafi yawan direbin ƙasar ke yi, musamman a lokutan bukuwan Kirsimeti,

Mista Biu ya gargadi direbobin da ke da wannan ɗabi’a da su tsayar da wannan hali nasu, ko su fuskanci fushin jami’an hukumar matuƙar suka je hannu.

A Najeriya ana samun yawaitar haɗuran mota a kan titunan ƙasar da ake yawan alaƙantawa da lalacewar htitunan ƙasar da kuma kauce wa dokokin tuƙi ciki har da gudun wuce kima da ma fi yawan direbobin ƙasar ke yi.

Categories
Siyasa

This is morning in kano Rabiu Musa Kwankwaso visit to the Hon Ghali Umar

Rabi’u Musa and Ghali Umar

This morning in Kano, I paid a condolence visit to the former Speaker of the House of Representatives, Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba who lost his mother, Hajiya Rabi, last week.

May Allah grant her soul eternal rest and make Jannatul Firdaus her final abode. – RMK

Categories
Siyasa

Who are the biggest influences in your life?

Design a site like this with WordPress.com
Get started