Categories
Labaran Duniya Nishadi Rahoto Siyasa Wasanni

Mutane 15 doka tasa halewa ayi musu jiniya a Najeriya -Abba Hikima

Duk Nigeria mutane 15 doka ta sahalewa yin amfani da jiniya. A ciki babu shugaban jami’an tsaro na farin kaya ballantana matar sa. Kuma hukuncin yin amfani da jiniya ga wanda doka bata sahalewa ba zaman gidan yari ne na wata 6.

Barin mutanen da basu cancanci a musu jiniya ba yin amfani da ita yana kara kumbura musu kai. Yana sa su girman kai da raina mutane. Kuma ya jawo raina doka.

Saboda haka, ya kamata yan sanda su kama wannan mata su gurfanar da ita a gaban kotu a bisa wannan laifi da sauran laifuffukan da suka fito fili.

Kuma indai shugabanni; zababbu da nadaddu basu takawa matan su da iyalan su birki akan shiga harkokin mulki ko bawa jami’an Nigeria umarni ba, to zaune bata kare mana ba a wannan kasa. Dan na tabbata wata rana wata shafaffiya-da-man in taci ta koshi, cewa za tayi a kamo mata shugaban sojoji.

Categories
Labaran Duniya

Sabuwar Gwamnati mai zuwa a Najeriya zata Gaji tiriliyan 77

Shugabar Ofishin Kula da Basuka a Najeriya Patience Oniha ta ce duk gwamnatin da za ta gaji ta Shugaba Muhammadu Buhari a ƙarshen watan Mayu za ta tarar da bashin da ya kai kusan naira tiriliyan 77.

Ta bayyana haka ne ranar Laraba yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da kasafin kuɗin ƙasar na 2023, wanda gwamnatin za ta cike giɓinsa ta hanyar ciyo bashi.

Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta ce za a samu kashi 22 cikin 100 na kuɗin shigar da aka yi hasashe ta hanyar cinikin man fetur, yayin da za a samu kashi 77 daga wasu harkokin daban.

Don cike giɓin, ministar ta ce sai an karɓo bashin naira tiriliyan 7.04 a cikin ƙasar da kuma tiriliyan 1.76 daga ƙasashen waje. Haka nan za a karɓo tiriliyan 1.77 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma sayar da kadarorin gwamnati da za su samar da naira biliyan 206.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan kasafin kuɗin na 2023 kan sama da naira tiriliyan 20, wanda ke da giɓin tiriliyan 11.

Categories
Labaran Duniya

Trump ya ƙaryata rahotan bayanan takardu biyan Harinji sa

Wani kwamitin majalisar dokokin Amurka ya fitar da bayanan haraji na tsohon shugaba Donald Trump na tsawon shekara shida.

Tsohon shugaban ya kwashe shekaru yana kokarin boye takardun – amma a watan jiya kotun kolin ta amince a bayyana su Bayanan harajin da kwamitin da yan jam’iyyar Democrat suka jagoranta sun nuna a cikin shekara guda, Mista Trump ya biya dala dari bakwai da hamsin kacal na haraji na gwamnatin tarayya, a wani lokacin kuma ba ya biyan komi.

Donald Trump ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa babu cikakkun bayanan da kowa zai iya fahimta. tare da sukar yan majalisar Democrat wadanda ya kira abin kunya ga majalisar Amurka

Categories
Labaran Duniya

A ƙalla mutum 20 suka Mutu sakamakon Haɗarin mota

Akalla mutum 20 ne suka mutu a wasu haɗuran mota biyu da suka auku a wurare biyu a Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta ƙasar Bisi Kazeem ya sanya wa hannu ya ce daya daga cikin haɗuran biyu ya auku ne a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yayin da ɗayan kuma ya auku a hanyar Mokwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutum 10 ne suka mutu a haɗarin hanyar Ibadan yayin da shida suka jikkata.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa wasu mutum 10 sun mutu a haɗarin da ya auku a hanyar Mokwa, tara nan take ɗaya kuma bayan an kai shi asibiti.

Sanarwar ta ambato muƙaddashin shugaban hukumar Dauda Biu na kokawa game da saɓa wa dokokin gudun wuce kima da mafi yawan direbin ƙasar ke yi, musamman a lokutan bukuwan Kirsimeti,

Mista Biu ya gargadi direbobin da ke da wannan ɗabi’a da su tsayar da wannan hali nasu, ko su fuskanci fushin jami’an hukumar matuƙar suka je hannu.

A Najeriya ana samun yawaitar haɗuran mota a kan titunan ƙasar da ake yawan alaƙantawa da lalacewar htitunan ƙasar da kuma kauce wa dokokin tuƙi ciki har da gudun wuce kima da ma fi yawan direbobin ƙasar ke yi.

Categories
Labaran Duniya

Ukraine na cikin Tsananin Buƙatar isar Gas da ma kaman Zelensky

Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya umarci ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ta G7 da su samar wa ƙasarsa ƙarin gas da makamai domin taimaka mata kuɓuta daga matsanancin sanyin da ke yin barazana ga rayuwar miliyoyin al’umar ƙasar da ke fama da hare-haren Rasha.

Sakamakon dusar ƙanƙara da ke ci gaba da sauka a wasu sassan ƙasar da kuma lalala tashar wutar lantarkin ƙasar da Rasha ta yi, mafi yawan al’umar ƙasar na fama matsanancin sanyi sakamakon rashin makamashin da za su ɗumama jikinsu da shi.

Yayin da yake jawabi ga taron ƙungiyar ta G7 ta bidiyo ranar Litinin, shugaba Zelensky ya ce Ukraine na buƙatar ”kusan cubic miliyan biyu” na gas a wannan lokacin na hunturu.

Ya kuma buƙaci ƙasashen da su aika wa Ukraine da ƙarin makamai ciki har da tankokin yaƙi da makaman atilari da makamai masu cin dogon zango.

Categories
Labaran Duniya

Volodymyr Zelensky ya tafi Amurka dan Ga nawa da Shugaban ƙasar Amurika Joe Biden

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya na kan hanyarsa ta zuwa Amurka, inda zai gana da shugaban kasar Joe Biden.

Wannan ce tafiyarsa ta farko da zai yi tun bayan da Rasha ta fara mamaya a kasarsa a watan Fabairun da ya wuce.

Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da ziyarar ta Mr Zelensky, ta na mai cewa za a ba wa Ukraine baturan makamai masu linzami don kara kare kasar daga hare haren Rasha.

Mr Zelensky dai na yawan karbar bakuncin shugabannin kasashen waje a Kyiv, sannan kuma ya na kai wa dakarunsa da ke sassan kasar ziyara akai-akai.

Amurka ita ce kasar da ta fi ba wa Ukraine taimakon makamai don mayar wa da Rasha martani.

Ana kuma ganin wannan ziyara za ta kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine.

Categories
Labaran Duniya

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da Kuɓutar da Wasu yan ƙasar China daga Hannun Masu garkuwa da Mutane


Gwamnatin jihar Neja ta sanar da kubutar da wasu ‘yan kasar Sin 7 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a wani wurin hakar ma’adinai da ke Ajata zuwa Aboki a karamar hukumar Shiroro ta jihar bayan kimanin watanni shida.

An yi garkuwa da Sinawan a ranar 29 ga watan Yuni na  2022 lokacin da daruruwan mahara cikin ayari  suka kai hari a wurin hakar ma’adinan inda aka kashe sojoji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar  da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar, ya ce rundunar sojojin sama ta ce ta gudanar da  aikin ceto mutanen.

Ya kara da cewa  an kubutar da ‘yan kasar ta Sin ne a wani yanki na karamar hukumar BirninGwari ta jihar 

Categories
Labaran Duniya

Mutum Goma sha biyu 12 su Mutu a ha ɗarin Mota

Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.

Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.

Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.

Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.

Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.

Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.

Categories
Labaran Duniya

Hukumomin a ƙasar Iran sun kama jarumar finafinan Alidoosti.

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin ƙasar da ake yi ta shiga wata na huɗu.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ƙarya da kuma ƙokarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta.

Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan.

A makonnin baya, ‘yar fim ɗin ta sanya wani hotonta a shafin sada zumunta babu ɗan-kwali tana kuma rike da allon alamar nuna goyon bayan zanga-zangar da ake yi a kasar.

Tauraruwar ta fito a cikin fim din da ya yi fice mai suna The Salesman.

Categories
Labaran Duniya

Najeriya ce tafi dacewa azo a zuba Hannun jari Muhammad Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da inga masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Washington DC yayin da yake wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka.

Yace baya ga yawan da kasar ke da shi bugu da kari tana da fadin kasa wanda shi ma wani abun tutiya ne, ya kuma ta zayyano wasu damarmaki da Najeriyan ke da su, wanda ya sa ta zama wurin da ya fi dacewa azuba hannun jari.

Cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ya fitar, ya ce “yana da matukar kyau in maimaita wannan, cewa Najeriya na da faffadan tattalin arziki.

Kuma na farko tana da yawan al’umma ita ce tafi kowacce kasar Afrika karfin tattalin arziki, babu shakka kuma Najeriya ce kan gaba wajen sayen kayayyaki da ake kai wa nahiyar.”

Design a site like this with WordPress.com
Get started