Categories
Labaran Duniya

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.

Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai da zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa’azinsa.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kare shi bai san shi ba kuma ba ya neman afuwa saboda, a cewarsa, bai aikata laifi ba don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Abduljabbar ya gaza kare da’awar da ya yi kan Annabi Muhammadu

Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa’azizzikan da ya sha gabatarwa, wadda kuma ake tuhumar sa a kanta, har da maganar cewa Annabi Muhammadu ya yi ƙwacen mata mai suna Safiyya daga wani sahabinsa.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce malamin “ya gaza kare wannan da’awa ko iƙirari da ya yi da karɓaɓɓun hujjoji”.

Ɗaya daga cikin lauyoyin gwamnatin Kano, Farfesa Mamman Lawan Yusufari, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun gabatar da shaidu huɗu don tabbatar da laifin da suke zargin malamin da shi.

Categories
Labaran Duniya

An tsinci gawar wata Budurwa a jahar Filato.

An tsinci gawar wata budurwa da aka jefar a Jos

Rahotanni daga garin Jos, babban birnin jihar Filato na cewa an tsinci gawar wata budurwa da aka jefar.

Budurwar da aka bayyana sunanta da Ruth an ga gawarta a wani wurin ‘wakin mota’ bayan wani gidan mai da ke kusa da gadar Farin Gada I, karamar hukumar Jos ta Arewa.

Sai dai alamu sun nuna cewa an yi wa mamaciyar fyade kafin a halakata har lahira.

Wata majiya ta bayyana cewa a jefar da gawar Ruth ne bayan an kashe ta a wani wuri na daban.

Jaridar Daily trust ta ce kafin hada rahotan kisan na Ruth ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar ta Filato Alabo Alfred amma ba su yi nasarar samunsa ba.

Categories
Labaran Duniya

‘Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin jihohin arewacin Nigeriya

Najeriya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a yankin Kolmani mai arzikin danyen mai

‘Yan bindiga sun addabi wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya. © dailypost

'Yan bindiga sun addabi wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya.

Makwanni kadan bayan da shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hako mai a sassan jihohin Bauchi da Gombe, yanzu haka wasu ‘yan bindiga sun fara addabar yankin ta hanyar hare-hare tare da sace–sacen mazauna Maimadi, da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Bayanai sun yi nuni da cewa kusan mutane 10 ne ya zuwa yanzu aka kashe tare da yin garkuwa da wasu da dama a yankin, kamar dai yadda za a ji a wannan rahoto da wakilinmu a Bauchi Ibrahim Malam Goje, ya aiko mana.

Tuni dai Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi cikin wata sanarwa da kakakinta SP Ahmed Wakil ya fitar, ta ce ta tura jami’anta don murkushe bata garin.

A nasu gefen, al’ummar yankin sun ce suna cikin mawuyacin hali.

Categories
Labaran Duniya

Iran ta ruguje rundunar ‘yan sandan tabbatar da Da’a ta ƙasar

Gwamnatin Iran ta sanar da soke bangaren jami’an ‘yan sandan tabbatar da da’a a Kasar, bayan zanga zangar da aka shafe kusan watanni 3 ana yi kan mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka zarga da keta dokkokin addini.

Zanga zangar da mata suka jagoranta a Iran, wadda hukumomi suka kira tarzoma ta yi sanadiyar dankwafar da al’amura a Kasar, tun bayan da Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 a duniya, ta gamu da ajalinta a ranar 16 ga watan Satumban da ya gabata, kwanaki 3 bayan jami’an ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a suka tsare ta.

Masu zanga zangar  sun kona hijabansu inda suke rera wakokin sukar gwamnati, abin da ya sa da dama daga cikin su suka daina amfani da hijabi musamman a wasu sassa na birnin Tehran

Kamfanin dillancin labaran Iran ISNA ya ruwaito Ministan shari’ar Kasar Mohammad Jafar Montazeri yana cewa rundunar ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a basu da damar zartar da hukunci a kan kowanene, saboda haka an soke su.

Kalaman Montazeri na zuwa ne a wani taron addini da aka gudanar, inda yake amsa tambayoyi a kan dalilin soke rundunar baki daya.

Zanga zangar dai ita ce irinta na farko cikin shekaru da dama a  Kasar,, wadda tayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 300, cikinsu har da jami’an tsaro.

Categories
Labaran Duniya

‘Yan bindiga sun daka wawa akan masallata A jahar Katsina

Zubin rubutu:@Yahaya Iliyasu

A Najeriya,  wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da masallata 19 bayan harbe limamin a wani hari da suka kai wani masallaci a jihar Katsina.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya ce Maharan sun far wa masallacin ne da ke kauyen Maigamji a jihar lokacin sallar magariba da yammacin Asabar, inda suka yi garkuwa da mutanen bayan sun harbe limamin tare da raunata wani mai ibada.

Gambo Isa ya ci gaba da cewa jami’an ‘yan sanda sun bi sawun wadannan ‘yan bindiga, kuma sun yi nasarar kubuto 6 daga cikinsu daga barayin, a yayin da ake ci gaba da kokakrin karbo saura 13 da sukaa rage.

Arewa maso yammaci da kuma maso tsakiyar Najeriya na fama da ayyukan masu aikata manyan laifuka da ake kira ‘yan bindiga, wadanda suke kai samame kauyuka, suna satar mutane da shanu don karbar kudin fansa, suna kuma kona gidaje bayan sun kwashe abubuwan da ke ciki.

A watan da ya gabata, mutane 15 ne ‘yan bindiga suka kashe, suka kuma raunata da dama a jerin hare haren da suka kai wasu kauyuka a jihar Kaduna da ke makwaftaka da Katsinar.

Categories
Labaran Duniya

Bazan ƙarancin Abinci ba a Najeriya-Buhari

Ministan noma da raya karkara na Najeriya Mohammed Abubakar ya yi watsi da fargabar da ake yi a kasar na fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin kasar, ministan ya ce ba za su bari hakan ta faru ba.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun bayyana cewa matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.

Sun kara da cewa an yi hasashen cewar kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.

To Amma ministan ya ce ”ba za mu bari matsalar karancin abinci ta yi tasiri a Najeriya ba, ina mai tabbatar muku da cewa da yardar Allah hakan ba za ta faru ba, saboda akwai matakai da dama da muka dauka domin magance wannan matsalar”.

Ya ci gaba da cewa ”daya daga cikin matakan da muka dauka shi ne noman rani, wanda muka ware masa kudi, muna aiki da ma’aikatar kudi, muna kuma samun tallafi daga cibiyoyin kudi, kamar bankin raya kasashen Afirka, dan haka za mu fadada noman ranin”.

Ministan ya kuma ce gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa. kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya ruwaito.

Article share tools

Categories
Labaran Duniya

Cutar ebola na barazanar dawo wa a Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun ce kasar na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola, da ake tunanin shigo da ita daga kasar Uganda.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta ce an samu karuwar baranazar barkewar cutar ne sakamakon yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cudanyar fasinjoji, musamman a filayen jiragen sama na Nairobi, da na Addis Ababa, da kuma filin jirgin sama na Kigali.

Hukumomin lafiyar kasar sun ce suna cikin shirin ko ta kwana, yayin da suka dauki matakan da suka dace domin yakar cutar idan ta barke.

Matakan sun hada da sanya ido kan fasinjoji tare da tantance su a filayen jiragen saman kasar.

Hukumar ta shawarci ‘yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda idan ba ta zama dole ba, daga yanzu zuwa wasu lokuta.

NCDC ta ce fasinjojin da suka zo kasar daga Uganda za a sanya ido a kansu na tsawon mako uku, domin tabbatar da halin da suke ciki.

An samu bullar cutar a kan mutum 100 tare da mutuwar mutum 30 a Uganda, tun bayan barkewarta a watan Satumba, ana kuma fargabar cewa cutar ka iya yaduwa zuwa makwabtan kasashe.

Categories
Labaran Duniya

Kada ku zaɓi wanda yace Gyaran Najeriya Abune mai Sauki.|Muhammdu Sunusi II

Yahaya Iliyasu

Sanusi Lamido Sanusi
Bayanan hoto,Muhammadu Sanusi ya ce “dole ne sai an shiga mawuyacin hali” kafin a gyara Najeriya

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi ‘yan ƙasar cewa gyaran Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, yana mai cewa duk ɗan takarar da ya faɗi akasin haka “ƙarya yake yi”.

Kazalika Sanusi, wanda sarkin Kano ne mai murabus, ya shawarci masu jefa ƙuri’a da kar su zaɓi duk ɗan siyasar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi.

“Matakan da za a ɗauka na gyara wannan [Najeriya] ba za su yi daɗi ba,” in ji shi yayin da yake magana a taron zuba jari da gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya ranar Asabar.

Taron ya samu halartar manyan baƙi kamar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da sauransu.

Haka nan, Ƙaramar Ministar Kasuwanci Mariam Yalwaji Katagum ce ta wakilci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wurin taron da ake kira KadInvest, wanda ake gudanarwa shekara-shekara karo na bakwai – 7.0.

‘Ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san aikin ba’

Muhammadu Sanusi
Bayanan hoto,Muhammadu Sanusi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna

Sanusi Lamido Sanusi – wanda a yanzu ake kira Muhammadu Sanusi – shi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna mai suna Kaduna Investment Promotion Agency.

Da yake gabatar da jawabinsa, tsohon gwamnan na CBN ya ce ganin yadda ake samun raguwa a kuɗaɗen haraji da kuma ɗumbin bashin da ake bin Najeriya, wajibi ne a ɗauki “matakai masu tsauri”.

“Matakan da za a ɗauka dole ne su zama masu tsauri. Saboda haka bari na shawarci ‘yan siyasarmu, dole ne ku faɗa wa ‘yan Najeriya gaskiya game da mawuyacin halin da za a shiga.

“Duk wanda ya faɗa muku cewa cikin sauƙi za a yi gyara kar ku zaɓe shi, saboda ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san irin aikin da ke gabansa ba.”

Sarkin na Kano mai murabus yana ganin cewa lallai sai an gyara tsarin biyan kuɗin lantarki da farashin man fetur, yana mai cewa “ana zuzuta yawan man da ‘yan Najeriya ke sha a kullum”.

A cewarsa: “Wajibi ne sai an ɗauki matakan da suka dace. Amma kafin a yi hakan, dole sai an gyara adadi na ƙarya da ake bayyanawa, sai an yaƙi cin hanci.”

Abin da sabon shugaban ƙasa ya kamata ya fara yi

Da ma an san Sanusi da ra’ayin goyon bayan cire tallafin man fetur, wanda bai gushe ba sai da ya yi kira ga duk wanda ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a 2023 da ya yi bincike a ɓangaren tallafin.

Ya ce: “Ina fatan duk wanda ya zama shugaban ƙasa a 2023, abin da zai fara yi shi ne ya nemi kamfanin mai na NNPC ya yi bayani kan duk dalar da ya karɓa a matsayin kuɗin tallafin mai.

“Dole ne su ba da bayanan jiragen ruwan da suka shigo wanda kuma za a iya tabbatarwa daga kamfanonin inshora ko da gaske ne jirgin ya sauka a Najeriya a wannan ranar.

Kar ku zaɓi duk ɗan takarar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi – Sanusi

“Saboda doka ta ce dole ne sai an nuna hujja kafin a karɓi kuɗin tallafi kuma dole ne sai an ba da hujja cewa an kawo man a kan farashin da mutum ya ce ya kawo shi. Haka doka ta ce.”

Tuni gwamnatin Buhari ta ce ta shirya daina biyan tallafin daga tsakiyar shekarar 2023, daidai lokacin da zai bar mulki bayan ya shafe wa’adi biyu na shekara takwas jimilla.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati na kashe fiye da naira tiriliyan ɗaya duk wata wajen biyan tallafin fetur, abin da masana tattalin arziki irin su Muhammadu Sanusi ke cewa gara a karkatar da su kan ayyukan raya ƙasa.

Categories
Labaran Duniya

An yiwa Ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ASUU Kishiya.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige
Bayanan hoto,Ministan Ƙwadago Chris Ngige ke nan yayin da yake miƙa wa shugabannin ƙungiyoyin NAMDA da CONUA

A ranar Talata ne gwamnatin Najeriya ta yi wa ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU kishiya da sabuwa mai suna Congress of Nigerian University Academics (CONUA) rijista, abin da ya jawo martani iri-iri daga ƙwararru da ma ‘yan ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bai wa National Association of Medical and Dental Academics (NAMDA) shaidar rijista, duka da zummar rage wa ASUU ƙarfin iko, kamar yadda masu sharhi ke cewa.

Mista Ngige ya ce ƙungiyoyin za su ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ASUU a jami’o’in ƙasar.

Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne yayin da kotu ta ba da umarnin a sasanta rikicin a wajen kotun gwamnati ta kai ƙarar ASUU gaban kotun ɗa’ar ma’aikata.

Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya zargi malaman jami’a da cin hanci da yin lalata da ɗalibai don ba su makin jarrabawa.

ASUU ta fara yajin aiki tun daga watan Fabarirun shekarar nan ta 2022 tana neman ƙarin albashi da kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i da kuma alawus-alawus.

Shahararren lauya mai gwagwarmayar kare haƙƙi, Femi Falana, ya ce rijistar da aka yi wa ƙungiyoyin ta saɓa wa doka.

A cewarsa, “dokar ƙwadago ta Najeriya ba ta ba da damar yi wa ƙungiya sama da ɗaya rijista a sashe ɗaya ba”.

Categories
Labaran Duniya

Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya wato NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a Unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi. Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a gidan . Ya bayyana cewa duka ƙwayoyin suna nauyin miligram 225. Mista Femi ya bayyana cewa gidan babu wani bil adama da ke zaune a ciki, sai dai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki. Ya kuma ce tuni aka kama wanda ake zargi da ajiye ƙwayoyin inda a halin yanzu yake hannun NDLEA. A ƴan kwanakin nan dai hukumar ta NDLEA na wawan kamu inda ko a kwanakin baya sai da ta kama hodar ibilis ta biliyoyin naira da kuma dubban kwalaben A-Kurkura da tabar wiwi a samame daban-daban da ta kai a fadin Najeriya. Article share tools Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya wato NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a Unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi. Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a gidan . Ya bayyana cewa duka ƙwayoyin suna nauyin miligram 225. Mista Femi ya bayyana cewa gidan babu wani bil adama da ke zaune a ciki, sai dai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki. Ya kuma ce tuni aka kama wanda ake zargi da ajiye ƙwayoyin inda a halin yanzu yake hannun NDLEA. A ƴan kwanakin nan dai hukumar ta NDLEA na wawan kamu inda ko a kwanakin baya sai da ta kama hodar ibilis ta biliyoyin naira da kuma dubban kwalaben A-Kurkura da tabar wiwi a samame daban-daban da ta kai a fadin Najeriya. Article share tools

NDLEA ta kama kwayoyin Tramol A jahar Legas
Design a site like this with WordPress.com
Get started