Categories
Labaran Duniya

Kada Jam’iyyun siyasa Sukar ɓi tallafin Kuɗaɗe daga Ƙasashen waje.

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bayyana cewa dole jam’iyyun ƙasar da aka yi wa rajista su bayyana inda suka samu kuɗin kamfe ɗinsu da kuma bin ƙa’idojin da aka gindaya na kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV a Najeriya inda ya ce akwai kuma adadin da aka ƙayyade na irin gudunmawar kuɗi da mutum zai iya bai wa jam’iyya a yaƙin neman zaɓe.

Haka kuma ya ƙara jaddada cewa jam’iyyu ba za su iya karɓar tallafin kuɗi ba daga ƙasashen waje.

A cewarsa, idan ma an samu irin wannan tallafin, ya zama dole a tura wa hukumar zabe waɗannan kuɗaɗe.

Categories
Labaran Duniya

An gudanar da zaɓen Yan majalisu a Bulgaria


Ana gudanar zaɓen ƴan majalisa a Bulgaria

Ana gudanar da zaɓe a ƙasar Bulgaria wanda wannan shi ne karo na huɗu da ake zaɓen ƴan majalisa a cikin watanni 18 a ƙasar.

Manyan abubuwan da za a mayar da hankali a kansu sun haɗa da hauhawar farashi da yaƙin Ukraine da wahalar makamashi da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Gwamnatocin haɗaka na baya sun sha fama da matsalolin da suka haɗa da cin hanci da rashawa.

Haka kuma akwai rabuwar kai tsakanin masu goyon bayan jam’iyyun da ke goyon bayan ƙasashen yamma da kuma masu goyon bayan Rasha.

Za a gudanar da wannan zaɓe ne bayan rushewar gwamnatin Kiril Petkov wadda ta shafe watanni shida kacal tana kan mulki.

Ƙoƙarin da ya yi na gyara albashi ya bi ruwa sakamakon hauhawar farashi.

Design a site like this with WordPress.com
Get started