Categories
Labaran Duniya

Ukraine na cikin Tsananin Buƙatar isar Gas da ma kaman Zelensky

Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya umarci ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ta G7 da su samar wa ƙasarsa ƙarin gas da makamai domin taimaka mata kuɓuta daga matsanancin sanyin da ke yin barazana ga rayuwar miliyoyin al’umar ƙasar da ke fama da hare-haren Rasha.

Sakamakon dusar ƙanƙara da ke ci gaba da sauka a wasu sassan ƙasar da kuma lalala tashar wutar lantarkin ƙasar da Rasha ta yi, mafi yawan al’umar ƙasar na fama matsanancin sanyi sakamakon rashin makamashin da za su ɗumama jikinsu da shi.

Yayin da yake jawabi ga taron ƙungiyar ta G7 ta bidiyo ranar Litinin, shugaba Zelensky ya ce Ukraine na buƙatar ”kusan cubic miliyan biyu” na gas a wannan lokacin na hunturu.

Ya kuma buƙaci ƙasashen da su aika wa Ukraine da ƙarin makamai ciki har da tankokin yaƙi da makaman atilari da makamai masu cin dogon zango.

Categories
Labaran Duniya

Volodymyr Zelensky ya tafi Amurka dan Ga nawa da Shugaban ƙasar Amurika Joe Biden

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya na kan hanyarsa ta zuwa Amurka, inda zai gana da shugaban kasar Joe Biden.

Wannan ce tafiyarsa ta farko da zai yi tun bayan da Rasha ta fara mamaya a kasarsa a watan Fabairun da ya wuce.

Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da ziyarar ta Mr Zelensky, ta na mai cewa za a ba wa Ukraine baturan makamai masu linzami don kara kare kasar daga hare haren Rasha.

Mr Zelensky dai na yawan karbar bakuncin shugabannin kasashen waje a Kyiv, sannan kuma ya na kai wa dakarunsa da ke sassan kasar ziyara akai-akai.

Amurka ita ce kasar da ta fi ba wa Ukraine taimakon makamai don mayar wa da Rasha martani.

Ana kuma ganin wannan ziyara za ta kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine.

Categories
Labaran Duniya

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da Kuɓutar da Wasu yan ƙasar China daga Hannun Masu garkuwa da Mutane


Gwamnatin jihar Neja ta sanar da kubutar da wasu ‘yan kasar Sin 7 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a wani wurin hakar ma’adinai da ke Ajata zuwa Aboki a karamar hukumar Shiroro ta jihar bayan kimanin watanni shida.

An yi garkuwa da Sinawan a ranar 29 ga watan Yuni na  2022 lokacin da daruruwan mahara cikin ayari  suka kai hari a wurin hakar ma’adinan inda aka kashe sojoji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar  da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar, ya ce rundunar sojojin sama ta ce ta gudanar da  aikin ceto mutanen.

Ya kara da cewa  an kubutar da ‘yan kasar ta Sin ne a wani yanki na karamar hukumar BirninGwari ta jihar 

Categories
Labaran Duniya

Mutum Goma sha biyu 12 su Mutu a ha ɗarin Mota

Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.

Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.

Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.

Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.

Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.

Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.

Categories
Wasanni

Filin wasa mafi girma dake ƙasar Qatar wanda za’a fafata wasan Ƙarshe a Yau

Wannan ƙaya tattun hotunan filin wasa da za a Ƙarƙare kasar cin kofin duniya a Dake ƙasar QATAR

Wannan ne filin wasa na Lusail Inda za’ayi fafa tawar ƙarshe a gasar cikin Duniya ta shekara 2022  tsakanin ƙasar Ajantina da ƙasar Faransa za a buga wannan wasan a Yau Lahadi da misalin karfe’ 4:00mp Agogon Najeriya Nijar Kamaru da ƙasar Chadi

Lusail filin wasane na musamman wanda a kafi Sani da  Lusail Iconics Stadium filin wasa mafi Girma a ƙasar Qatar wanda yake cin Mutane sama da dubu 80,000 kuma na da nisan kilomita Ɗaya 1 wanda ka gina da Kwanon gwal  tare da talafin durakun  Ƙarfe 24.

Categories
Labaran Duniya

Hukumomin a ƙasar Iran sun kama jarumar finafinan Alidoosti.

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin ƙasar da ake yi ta shiga wata na huɗu.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ƙarya da kuma ƙokarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta.

Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan.

A makonnin baya, ‘yar fim ɗin ta sanya wani hotonta a shafin sada zumunta babu ɗan-kwali tana kuma rike da allon alamar nuna goyon bayan zanga-zangar da ake yi a kasar.

Tauraruwar ta fito a cikin fim din da ya yi fice mai suna The Salesman.

Categories
Labaran Duniya

Najeriya ce tafi dacewa azo a zuba Hannun jari Muhammad Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da inga masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Washington DC yayin da yake wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka.

Yace baya ga yawan da kasar ke da shi bugu da kari tana da fadin kasa wanda shi ma wani abun tutiya ne, ya kuma ta zayyano wasu damarmaki da Najeriyan ke da su, wanda ya sa ta zama wurin da ya fi dacewa azuba hannun jari.

Cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ya fitar, ya ce “yana da matukar kyau in maimaita wannan, cewa Najeriya na da faffadan tattalin arziki.

Kuma na farko tana da yawan al’umma ita ce tafi kowacce kasar Afrika karfin tattalin arziki, babu shakka kuma Najeriya ce kan gaba wajen sayen kayayyaki da ake kai wa nahiyar.”

Categories
Labaran Duniya

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.

Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai da zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa’azinsa.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kare shi bai san shi ba kuma ba ya neman afuwa saboda, a cewarsa, bai aikata laifi ba don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Abduljabbar ya gaza kare da’awar da ya yi kan Annabi Muhammadu

Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa’azizzikan da ya sha gabatarwa, wadda kuma ake tuhumar sa a kanta, har da maganar cewa Annabi Muhammadu ya yi ƙwacen mata mai suna Safiyya daga wani sahabinsa.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce malamin “ya gaza kare wannan da’awa ko iƙirari da ya yi da karɓaɓɓun hujjoji”.

Ɗaya daga cikin lauyoyin gwamnatin Kano, Farfesa Mamman Lawan Yusufari, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun gabatar da shaidu huɗu don tabbatar da laifin da suke zargin malamin da shi.

Categories
Nishadi

Na taɓa samu kyautar Naira miliyan Arba’in-(40m)

An taba bani kyautar kudi N40m inji wata ‘yar fim

Tauraruwar fina-finan kudancin Nijeriya Nollywood Toyin Abraham ta ce tana matukar kaunar bayyana a Talabijin domin nishadantar da mutane ba wai don ta samu kudi ba.

Tauraruwar da ta bayyana a cikin shirin ‘Rubbin Minds’ na gidan Talabijin na Channels, ta ce a harkar fim ta samu kudi ta yi arziki a saukake.

‘Yar kimanin shekaru 40, Toyin Abraham ta ce ta fara samun kudi a harkar fim shekaru 5 da suka gabata. Ta ce bata mantawa lokacin da aka kira ta a waya don ta tura lambar bankin ta.

Bayan tura lambar bankin ne ta ga kamar a mafarki, an tura mata kudi jibge har Naira milyan 40, inda ta ce hakan sai da ya sa bacci ya gagare ta.

Categories
Siyasa

Yan bindiga sun tashi ofishin jam’iyyar PDP a Gombe.

Jamiyyar PDP mai hammaya a jihar Gombe ta ce wasu da ake zargim yan bangar siyasa sun cina wuta a ofishin yakin neman zaben dan takararta na gwamnan jihar Mohamed Barde da tsakar daren Litinin.

PDP ta kuma ce wannan ba shi ne karon farko da ake kai wa ofishinta hari ba.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce ta soma gudanar da bincike a kan lamarin.

Babu dai cikakkun bayanai kan harin, amma dai PDP ta zargi APC da wannan hari.

A sanarwar da ta fitar, Mohammed Barde ya ce sun tafka asara sosai a harin.

Sai dai babban jami’in yada labaran gwamna mai ci Inuwa Yahaya, ya ce PDP kawai na neman abin tallata kansu ne.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce sun kaddamar da bincike kan lamarin.

Design a site like this with WordPress.com
Get started