Categories
Labaran Duniya

An tsinci gawar wata Budurwa a jahar Filato.

An tsinci gawar wata budurwa da aka jefar a Jos

Rahotanni daga garin Jos, babban birnin jihar Filato na cewa an tsinci gawar wata budurwa da aka jefar.

Budurwar da aka bayyana sunanta da Ruth an ga gawarta a wani wurin ‘wakin mota’ bayan wani gidan mai da ke kusa da gadar Farin Gada I, karamar hukumar Jos ta Arewa.

Sai dai alamu sun nuna cewa an yi wa mamaciyar fyade kafin a halakata har lahira.

Wata majiya ta bayyana cewa a jefar da gawar Ruth ne bayan an kashe ta a wani wuri na daban.

Jaridar Daily trust ta ce kafin hada rahotan kisan na Ruth ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar ta Filato Alabo Alfred amma ba su yi nasarar samunsa ba.

Categories
Labaran Duniya

‘Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin jihohin arewacin Nigeriya

Najeriya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a yankin Kolmani mai arzikin danyen mai

‘Yan bindiga sun addabi wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya. © dailypost

'Yan bindiga sun addabi wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya.

Makwanni kadan bayan da shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hako mai a sassan jihohin Bauchi da Gombe, yanzu haka wasu ‘yan bindiga sun fara addabar yankin ta hanyar hare-hare tare da sace–sacen mazauna Maimadi, da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Bayanai sun yi nuni da cewa kusan mutane 10 ne ya zuwa yanzu aka kashe tare da yin garkuwa da wasu da dama a yankin, kamar dai yadda za a ji a wannan rahoto da wakilinmu a Bauchi Ibrahim Malam Goje, ya aiko mana.

Tuni dai Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi cikin wata sanarwa da kakakinta SP Ahmed Wakil ya fitar, ta ce ta tura jami’anta don murkushe bata garin.

A nasu gefen, al’ummar yankin sun ce suna cikin mawuyacin hali.

Categories
Siyasa

Yan bindiga sun yi dirar Mikiya a gidan shugaban kwamitin yaƙin Zaɓen PDP

‘Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Lee Maeba a jihar Ribas.

Sun lalata motoci sama da biyar a gidan, a harin da suka kai jiya Alhamis da safe.

Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP a Ribas, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels faruwar lamarin, inda ya ce wani mutumi ne ya kira sa tare da fada masa cewa ya yi taka tsan-tsan kan yunkurin kawo harin.

Ya ce an kawo harin ne jim kadan bayan fitar sa zuwa gidan surukansa, inda suka yi ta harbe-harbe a kofar gidan tare da daure maigadin gidan.

An ruwaito raunata mutum akalla uku yayin harin.

Babu wata sanarwa daga wajen ‘yan sanda kan harin lokacin hada rahoton, sai dai, gwamnatin Ribas ta umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin.

Article share tools

Categories
Labaran Duniya

Iran ta ruguje rundunar ‘yan sandan tabbatar da Da’a ta ƙasar

Gwamnatin Iran ta sanar da soke bangaren jami’an ‘yan sandan tabbatar da da’a a Kasar, bayan zanga zangar da aka shafe kusan watanni 3 ana yi kan mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka zarga da keta dokkokin addini.

Zanga zangar da mata suka jagoranta a Iran, wadda hukumomi suka kira tarzoma ta yi sanadiyar dankwafar da al’amura a Kasar, tun bayan da Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 a duniya, ta gamu da ajalinta a ranar 16 ga watan Satumban da ya gabata, kwanaki 3 bayan jami’an ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a suka tsare ta.

Masu zanga zangar  sun kona hijabansu inda suke rera wakokin sukar gwamnati, abin da ya sa da dama daga cikin su suka daina amfani da hijabi musamman a wasu sassa na birnin Tehran

Kamfanin dillancin labaran Iran ISNA ya ruwaito Ministan shari’ar Kasar Mohammad Jafar Montazeri yana cewa rundunar ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a basu da damar zartar da hukunci a kan kowanene, saboda haka an soke su.

Kalaman Montazeri na zuwa ne a wani taron addini da aka gudanar, inda yake amsa tambayoyi a kan dalilin soke rundunar baki daya.

Zanga zangar dai ita ce irinta na farko cikin shekaru da dama a  Kasar,, wadda tayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 300, cikinsu har da jami’an tsaro.

Categories
Siyasa

Ko dan magoya bayan ka rege kuɗin shiga jami’ar ka – Sen.Kwankwaso

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya roki abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya rage kudin makaranta a jami’arsa, wanda dubban ‘yan Najeriya magoya bayansa zasu samu damar samun ilimi.

Kwankwaso ya bayyana haka ne ranar Lahadi yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda za a inganta bangaren ilimi a wani taron da gidan Talabijin na Arise TV ta gayyacesu tare da hadin guiwar cibiyar damokaradiyya da cigaba da jaridar Vanguard.

“Dole ne inyi godiya ga Waziri, yana da jami’a wacce take da kyau sosai. Abu daya da ya dace yayi kokarin yi shi ne ya yi kasa da kudin makarantar ta yadda magoya bayansa da ‘yan Najeriya masu yawa zasu iya shiga.”

Kwankwaso ya kara da cewa, zai karfafa bangarori masu zaman kansu da su zuba hannayen jari a fannin ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a yayin da yace komai dangane da ASUU dole ne ya zamo na gaskiya.

A yayin amsa tambayar, Atiku ya tsaya kan cewa ilimi yafi komai amfani cikin abubuwan da ya dace yara su samu ta yadda za a habaka cigaban kasa yayin da ya jaddada cewa a zuba kudi masu yawa a bangaren ilimi.

“Abu mafi muhimmanci shi ne a ilimantar da yaranmu. Kuma ba ilimi kawai ba, yadda ya dace. Daga nan ne zasu iya bada gudumawa a fannin cigaban bangaren wanda shi ne tushen tattalin arziki.”

Atiku ya kara da bada misali kan yadda aka kirkiro UBEC yayin da yake mataimakin shugaban kasa wanda ya zama wajibi ga kowanne yaro ‘dan Najeriya da ya samu ilimin firamare zuwa karamar sakandare kyauta.

Jami’ar Amurka (ABTI) dake Najeriya a garin Yola dake jihar Adamawa, mallakin Atiku Abubakar ce, jaridar Vanguard ta rahoto

Categories
Wasanni

Da yiwuwar ɗan wasa Neymar ka iya buga kasar cin kofin Duniya

Watakila Neymar ya buga wasan da Brazil za ta fafata da Koriya ta Kudu ranar Litinin a karawar zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar.

Mai shekara 30 bai yi wa Brazil wasan da ta ci Switzerland ba da wanda Kamaru ta yi nasara a fafatawar cikin rukuni na bakwai.

Dan kwallon mai taka leda a Paris St Germain ya ji rauni a wasan farko a cikin rukuni da Brazil ta ci Serbia 2-0.

Brazil wadda ake sa ran za ta iya daukar kofin Qatar ta kai zaga na biyu tun kan ta fuskanci Kamaru a wasan karshe a rukuni na bakwai.

Koriya ta Kudu kuwa ta yi ta biyu ne a rukuni na takwas da maki hudu.

Wannan shi ne wasa na takwas da za a kece raini tsakanin tawagogin biyu, amma na farko a babbar Gasar tamaula ta Duniya.

Brazil ta yi nasara a wasa shida aka doke ta karawa daya – wasan karshe da suka fuskanci juna shi ne a watan Yuni, inda Brazil ta ci 5-1.

Duk wadda ta yi nasara a wasan Litinin za ta buga daf da na kusa da na karshe tsakanin Japan da Croatia.

Croatia ita ta yi ta biyu a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Rasha a 2018, wanda Faransa ta lashe.

Categories
Labaran Duniya

‘Yan bindiga sun daka wawa akan masallata A jahar Katsina

Zubin rubutu:@Yahaya Iliyasu

A Najeriya,  wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da masallata 19 bayan harbe limamin a wani hari da suka kai wani masallaci a jihar Katsina.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya ce Maharan sun far wa masallacin ne da ke kauyen Maigamji a jihar lokacin sallar magariba da yammacin Asabar, inda suka yi garkuwa da mutanen bayan sun harbe limamin tare da raunata wani mai ibada.

Gambo Isa ya ci gaba da cewa jami’an ‘yan sanda sun bi sawun wadannan ‘yan bindiga, kuma sun yi nasarar kubuto 6 daga cikinsu daga barayin, a yayin da ake ci gaba da kokakrin karbo saura 13 da sukaa rage.

Arewa maso yammaci da kuma maso tsakiyar Najeriya na fama da ayyukan masu aikata manyan laifuka da ake kira ‘yan bindiga, wadanda suke kai samame kauyuka, suna satar mutane da shanu don karbar kudin fansa, suna kuma kona gidaje bayan sun kwashe abubuwan da ke ciki.

A watan da ya gabata, mutane 15 ne ‘yan bindiga suka kashe, suka kuma raunata da dama a jerin hare haren da suka kai wasu kauyuka a jihar Kaduna da ke makwaftaka da Katsinar.

Categories
Siyasa

Idan Na zama Shugaban Najeriya dukkanin jarabawar da za a Biya kuɗi zasu Zana ta Kyauta-Kwankwaso

ikin kundin manufofin takararsa ta shugaban ƙasa (Blueprint) dan takarar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jarabawowin kammala karatun sikandire a Nigeria da suka hada da NECO, WAEC, NABTEBE, NBAIS, duk zasu kasance kyauta ne ga dalibai a Nigeria, idan har ya zama shugaban ƙasa.

Kwankwaso yana taron ƙaddamar da jadawalin kundin manufofin takararsa yau a babban birnin tarayyar Abuja, inda yace za’a kara wa’adin jarabawar neman gurbin shiga jami’a ta JAMB zuwa shekaru hudu kafin ta daina aiki.

Saura bayanai nanan tafe…

Categories
Labaran Duniya

Bazan ƙarancin Abinci ba a Najeriya-Buhari

Ministan noma da raya karkara na Najeriya Mohammed Abubakar ya yi watsi da fargabar da ake yi a kasar na fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin kasar, ministan ya ce ba za su bari hakan ta faru ba.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun bayyana cewa matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.

Sun kara da cewa an yi hasashen cewar kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.

To Amma ministan ya ce ”ba za mu bari matsalar karancin abinci ta yi tasiri a Najeriya ba, ina mai tabbatar muku da cewa da yardar Allah hakan ba za ta faru ba, saboda akwai matakai da dama da muka dauka domin magance wannan matsalar”.

Ya ci gaba da cewa ”daya daga cikin matakan da muka dauka shi ne noman rani, wanda muka ware masa kudi, muna aiki da ma’aikatar kudi, muna kuma samun tallafi daga cibiyoyin kudi, kamar bankin raya kasashen Afirka, dan haka za mu fadada noman ranin”.

Ministan ya kuma ce gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa. kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya ruwaito.

Article share tools

Categories
Labaran Duniya

Cutar ebola na barazanar dawo wa a Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun ce kasar na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola, da ake tunanin shigo da ita daga kasar Uganda.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta ce an samu karuwar baranazar barkewar cutar ne sakamakon yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cudanyar fasinjoji, musamman a filayen jiragen sama na Nairobi, da na Addis Ababa, da kuma filin jirgin sama na Kigali.

Hukumomin lafiyar kasar sun ce suna cikin shirin ko ta kwana, yayin da suka dauki matakan da suka dace domin yakar cutar idan ta barke.

Matakan sun hada da sanya ido kan fasinjoji tare da tantance su a filayen jiragen saman kasar.

Hukumar ta shawarci ‘yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda idan ba ta zama dole ba, daga yanzu zuwa wasu lokuta.

NCDC ta ce fasinjojin da suka zo kasar daga Uganda za a sanya ido a kansu na tsawon mako uku, domin tabbatar da halin da suke ciki.

An samu bullar cutar a kan mutum 100 tare da mutuwar mutum 30 a Uganda, tun bayan barkewarta a watan Satumba, ana kuma fargabar cewa cutar ka iya yaduwa zuwa makwabtan kasashe.

Design a site like this with WordPress.com
Get started