Categories
Siyasa

EU ta sake saka takunkumi akan Rasha da zai shafi Man da take fitarwa.

Majalisar gudanarwar Turai. AP – Jean-Francois Badias

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sake kakaba wasu kunshin takunkuman karya tattalin arziki kan Rasha dangane da abin da ta ke aikatawa a Ukraine, cikin takunkuman har da wanda ya kayyade farashin mai da kuma hana fitar da kayayyakin da Moscow ke yi na kusan yuro biliyan bakwai.

Shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen ta ce takunmuman sun kuma kunshi hana wasu da ke taimakawa Rasha tafiye-tafiye da kuma kama wasu kaddarorin su.

Kunshin takunkuman sun kuma haramtawa turawa zama mamba a kwamitocin gudanarwar kamfanoni mallakar gwamnatin Rasha.

Shima jami’in kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Josep Borrell, ya ce mutanen da wannan takunkumi ya shafa sun hada da wadanda ke taimakawa Moscow wajen kaucewa takunkumin da aka sanya mata.

Tun a watan Mayun da ya gabata, kungiyar ta EU ta amince da haramta shigar da mafi yawan man Rasha zuwa nahiyar.

Yunkurin kara farashin man da EU ta yi, na nufin kayyade yawan kudaden da kasashe irin su China da India ke biya na danyen man Rasha. Tushen wannan labari daga RFI Hausa.

Categories
Siyasa

Buhari ya a Mince da A siyawa NDLEA Mutoci masu Sulki.

Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe naira miliyan N580.5 don sayo motoci masu silke da zimmar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA).ke yi.

NDLEA na ƙarƙashin kulawar ofishin Ma’aikatar Shari’a wadda kuma ita ce ta gabatar da ƙudirin neman sayen motocin, kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na yau Laraba.

A cewarsa: “Daliln da ya sa aka gabatar da ƙudirin shi ne don a nemi amincewar majalisar wajen bayar da kwangilar sayo motoci huɗu masu silke da ke da kujeru 14 ga NDLEA.”

Ya ƙara da cewa an yanke shawarar sayo motocin ne da zimmar kare rayuwar jami’an hukumar ta NDLEA “da ke aiki tuƙuru don ba da sakamako mai kyau”.

Kuɗin sun ƙunshi kashi 7.5 cikin 100 na kuɗin harajin VAT na tsawon mako 16, a cewar ministan.

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun Fara yaƙin Neman zaben shugaban kasa

Yau laraba 28 ga watan Satumba ne ranar da aka sahalewa ‘yan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya fara gangamin yakin neman zabe, don tunkarar  zaben kasar na shekarar 2023.

‘Yan takara 18 da ke neman darewa kujerar shugabancin Najeriya, za su shawo kan mutane miliyan 96 da dubu 300 don kada musu kuri’a a zaben na ranar 25 ga watan Fabarairu da nufin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari.

Tun farko hukumar zaben Najeriya INEC ce ta ware ranar ta yau don sahalewa ‘yan takarar kaddamar da yakin neman zabensu.  

Jerin ‘yan takarar shugaban kasar da za su fafata a zaben na 2023 sun hada da Imumolen Christopher na AP kana Al Mustapha Hamza na AA sai Omoyele Sowore na AAC Kachikwu Dumebi na ADC sannan dan takarar jam’iyyar ADP Sani Yabagi tukuna Bola Ahmed Tunibu na jam’iyya mai mulki APC.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Umeadi Chukwudi na APGA sannan Ojei Princess daga APM sai Nnadi Osita daga APP akwai kuma Adenuga Oluwafemi na BP SANNAN Peter Obi daga LP da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso daga NNPP.

Kamar yadda kunshin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar ya nuna, jam’iyyar NRM na da nata dan takarar Osakwe Johnson yayinda Atiku Abubakar ke tsayawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP yayinda Abiola Kolawole ke yiwa PRP takara sai kuma Adebayo Adewole na SDP kana Ado-Ibrahim Abdulmalik daga YPP tukuna dan takarar jam’iyyar ZLP Dan Nwanyanwu.

Kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna, za a gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun tarayya ranar asabar 25 ga watan Fabarairun 2023 kana ayi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a ranar 11 ga watan Maris wato makwanni 2 tsakani.

Ga duk wanda ya yi nasara a tsakanin ‘yan takarar 18 za a rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriyar ranar 29 ga watan Mayun shekarar ta

Design a site like this with WordPress.com
Get started