Categories
Labaran Duniya

A ƙalla mutum 20 suka Mutu sakamakon Haɗarin mota

Akalla mutum 20 ne suka mutu a wasu haɗuran mota biyu da suka auku a wurare biyu a Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta ƙasar Bisi Kazeem ya sanya wa hannu ya ce daya daga cikin haɗuran biyu ya auku ne a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yayin da ɗayan kuma ya auku a hanyar Mokwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutum 10 ne suka mutu a haɗarin hanyar Ibadan yayin da shida suka jikkata.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa wasu mutum 10 sun mutu a haɗarin da ya auku a hanyar Mokwa, tara nan take ɗaya kuma bayan an kai shi asibiti.

Sanarwar ta ambato muƙaddashin shugaban hukumar Dauda Biu na kokawa game da saɓa wa dokokin gudun wuce kima da mafi yawan direbin ƙasar ke yi, musamman a lokutan bukuwan Kirsimeti,

Mista Biu ya gargadi direbobin da ke da wannan ɗabi’a da su tsayar da wannan hali nasu, ko su fuskanci fushin jami’an hukumar matuƙar suka je hannu.

A Najeriya ana samun yawaitar haɗuran mota a kan titunan ƙasar da ake yawan alaƙantawa da lalacewar htitunan ƙasar da kuma kauce wa dokokin tuƙi ciki har da gudun wuce kima da ma fi yawan direbobin ƙasar ke yi.

Categories
Wasanni

Pogba yace ba zai Bugawa Faransa Gasar Kofin duniya ba

Dan wasan Juventus, Paul Pogba ba zai buga wa Faransa gasar cin kofin duniya a Qatar, bayan da bai murmure daga jinyar gwiwar kafa ba.

Pogba mai shekara 29, bai yi wasa ko daya ba a Serie A ta kakar nan, tun bayan da ya sake komawa Juventus daga Manchester United a kakar nan.

Ya ji raunin a gwiwar kafarsa a cikin watan Yuli, wanda bai amince a yi masa aiki ba a lokacin don gudan kada ya kasa zuwa gasar kofin duniya.

Qatar za ta karbi bakuncin babbar gasar tamaula ta duniya daga ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Faransa mai rike da kofin za ta fara wasa da Australia ranar 22 ga watan Nuwamba.

Pogba wanda rabon da ya yi wa Faransa tamaula tun bayan doke Afirka ta Kudu 5-0 a wasan sada zumunta cikin watan Maris, ya koma atisaye a farkon watan jiya.

Amma sai ya kasa motsa jiki yadda ya kamata, hakan ya sa ya yanke shawarar da likitoci su yi masa tiyatar.

Tawagar Faransa ta lashe kofin duniya a Rasha a 2018 tare da Pogba a lokacin.

Categories
Labaran Duniya

Kada ku zaɓi wanda yace Gyaran Najeriya Abune mai Sauki.|Muhammdu Sunusi II

Yahaya Iliyasu

Sanusi Lamido Sanusi
Bayanan hoto,Muhammadu Sanusi ya ce “dole ne sai an shiga mawuyacin hali” kafin a gyara Najeriya

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi ‘yan ƙasar cewa gyaran Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, yana mai cewa duk ɗan takarar da ya faɗi akasin haka “ƙarya yake yi”.

Kazalika Sanusi, wanda sarkin Kano ne mai murabus, ya shawarci masu jefa ƙuri’a da kar su zaɓi duk ɗan siyasar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi.

“Matakan da za a ɗauka na gyara wannan [Najeriya] ba za su yi daɗi ba,” in ji shi yayin da yake magana a taron zuba jari da gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya ranar Asabar.

Taron ya samu halartar manyan baƙi kamar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da sauransu.

Haka nan, Ƙaramar Ministar Kasuwanci Mariam Yalwaji Katagum ce ta wakilci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wurin taron da ake kira KadInvest, wanda ake gudanarwa shekara-shekara karo na bakwai – 7.0.

‘Ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san aikin ba’

Muhammadu Sanusi
Bayanan hoto,Muhammadu Sanusi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna

Sanusi Lamido Sanusi – wanda a yanzu ake kira Muhammadu Sanusi – shi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna mai suna Kaduna Investment Promotion Agency.

Da yake gabatar da jawabinsa, tsohon gwamnan na CBN ya ce ganin yadda ake samun raguwa a kuɗaɗen haraji da kuma ɗumbin bashin da ake bin Najeriya, wajibi ne a ɗauki “matakai masu tsauri”.

“Matakan da za a ɗauka dole ne su zama masu tsauri. Saboda haka bari na shawarci ‘yan siyasarmu, dole ne ku faɗa wa ‘yan Najeriya gaskiya game da mawuyacin halin da za a shiga.

“Duk wanda ya faɗa muku cewa cikin sauƙi za a yi gyara kar ku zaɓe shi, saboda ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san irin aikin da ke gabansa ba.”

Sarkin na Kano mai murabus yana ganin cewa lallai sai an gyara tsarin biyan kuɗin lantarki da farashin man fetur, yana mai cewa “ana zuzuta yawan man da ‘yan Najeriya ke sha a kullum”.

A cewarsa: “Wajibi ne sai an ɗauki matakan da suka dace. Amma kafin a yi hakan, dole sai an gyara adadi na ƙarya da ake bayyanawa, sai an yaƙi cin hanci.”

Abin da sabon shugaban ƙasa ya kamata ya fara yi

Da ma an san Sanusi da ra’ayin goyon bayan cire tallafin man fetur, wanda bai gushe ba sai da ya yi kira ga duk wanda ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a 2023 da ya yi bincike a ɓangaren tallafin.

Ya ce: “Ina fatan duk wanda ya zama shugaban ƙasa a 2023, abin da zai fara yi shi ne ya nemi kamfanin mai na NNPC ya yi bayani kan duk dalar da ya karɓa a matsayin kuɗin tallafin mai.

“Dole ne su ba da bayanan jiragen ruwan da suka shigo wanda kuma za a iya tabbatarwa daga kamfanonin inshora ko da gaske ne jirgin ya sauka a Najeriya a wannan ranar.

Kar ku zaɓi duk ɗan takarar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi – Sanusi

“Saboda doka ta ce dole ne sai an nuna hujja kafin a karɓi kuɗin tallafi kuma dole ne sai an ba da hujja cewa an kawo man a kan farashin da mutum ya ce ya kawo shi. Haka doka ta ce.”

Tuni gwamnatin Buhari ta ce ta shirya daina biyan tallafin daga tsakiyar shekarar 2023, daidai lokacin da zai bar mulki bayan ya shafe wa’adi biyu na shekara takwas jimilla.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati na kashe fiye da naira tiriliyan ɗaya duk wata wajen biyan tallafin fetur, abin da masana tattalin arziki irin su Muhammadu Sanusi ke cewa gara a karkatar da su kan ayyukan raya ƙasa.

Categories
Siyasa

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun Fara yaƙin Neman zaben shugaban kasa

Yau laraba 28 ga watan Satumba ne ranar da aka sahalewa ‘yan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya fara gangamin yakin neman zabe, don tunkarar  zaben kasar na shekarar 2023.

‘Yan takara 18 da ke neman darewa kujerar shugabancin Najeriya, za su shawo kan mutane miliyan 96 da dubu 300 don kada musu kuri’a a zaben na ranar 25 ga watan Fabarairu da nufin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari.

Tun farko hukumar zaben Najeriya INEC ce ta ware ranar ta yau don sahalewa ‘yan takarar kaddamar da yakin neman zabensu.  

Jerin ‘yan takarar shugaban kasar da za su fafata a zaben na 2023 sun hada da Imumolen Christopher na AP kana Al Mustapha Hamza na AA sai Omoyele Sowore na AAC Kachikwu Dumebi na ADC sannan dan takarar jam’iyyar ADP Sani Yabagi tukuna Bola Ahmed Tunibu na jam’iyya mai mulki APC.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Umeadi Chukwudi na APGA sannan Ojei Princess daga APM sai Nnadi Osita daga APP akwai kuma Adenuga Oluwafemi na BP SANNAN Peter Obi daga LP da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso daga NNPP.

Kamar yadda kunshin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar ya nuna, jam’iyyar NRM na da nata dan takarar Osakwe Johnson yayinda Atiku Abubakar ke tsayawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP yayinda Abiola Kolawole ke yiwa PRP takara sai kuma Adebayo Adewole na SDP kana Ado-Ibrahim Abdulmalik daga YPP tukuna dan takarar jam’iyyar ZLP Dan Nwanyanwu.

Kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna, za a gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun tarayya ranar asabar 25 ga watan Fabarairun 2023 kana ayi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a ranar 11 ga watan Maris wato makwanni 2 tsakani.

Ga duk wanda ya yi nasara a tsakanin ‘yan takarar 18 za a rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriyar ranar 29 ga watan Mayun shekarar ta

Design a site like this with WordPress.com
Get started