Categories
Siyasa

Mun samu tattaunawa da Shugaban jam’iyar NNPP Na jahar Kano-Magaji Rimin Godo

Tsohon dakataccen shugaban hukumar karbar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa, sun tattauna da shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, da kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Rimin Gado, domin ganin yadda za’a ciyar da Kano gaba.

Cikin wani saƙo da ya wallafa yau a shafinsa na sada zumunta, an hangi fuskokinsu cike da annuri da walwala.

Muhuyi dai ya fice daga jam’iyyar APC bayan wata tashin-tashina da ta faru tsakaninsa da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya kowa jam’iyyar PDP har ya siyo tikitin neman takarar gwamnan Kano.

Sauran bayanai nanan tafe…

Categories
Labaran Duniya

Kada Jam’iyyun siyasa Sukar ɓi tallafin Kuɗaɗe daga Ƙasashen waje.

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bayyana cewa dole jam’iyyun ƙasar da aka yi wa rajista su bayyana inda suka samu kuɗin kamfe ɗinsu da kuma bin ƙa’idojin da aka gindaya na kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV a Najeriya inda ya ce akwai kuma adadin da aka ƙayyade na irin gudunmawar kuɗi da mutum zai iya bai wa jam’iyya a yaƙin neman zaɓe.

Haka kuma ya ƙara jaddada cewa jam’iyyu ba za su iya karɓar tallafin kuɗi ba daga ƙasashen waje.

A cewarsa, idan ma an samu irin wannan tallafin, ya zama dole a tura wa hukumar zabe waɗannan kuɗaɗe.

Categories
Labaran Duniya

An gudanar da zaɓen Yan majalisu a Bulgaria


Ana gudanar zaɓen ƴan majalisa a Bulgaria

Ana gudanar da zaɓe a ƙasar Bulgaria wanda wannan shi ne karo na huɗu da ake zaɓen ƴan majalisa a cikin watanni 18 a ƙasar.

Manyan abubuwan da za a mayar da hankali a kansu sun haɗa da hauhawar farashi da yaƙin Ukraine da wahalar makamashi da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Gwamnatocin haɗaka na baya sun sha fama da matsalolin da suka haɗa da cin hanci da rashawa.

Haka kuma akwai rabuwar kai tsakanin masu goyon bayan jam’iyyun da ke goyon bayan ƙasashen yamma da kuma masu goyon bayan Rasha.

Za a gudanar da wannan zaɓe ne bayan rushewar gwamnatin Kiril Petkov wadda ta shafe watanni shida kacal tana kan mulki.

Ƙoƙarin da ya yi na gyara albashi ya bi ruwa sakamakon hauhawar farashi.

Categories
Siyasa

Korea ta Arewa ta sake Gwajin makami mai linzami.

Koriya ta Arewa ta sake harba makamai ma su linzami guda biyu zuwa Tekun Gabashin Chaina, kwanaki biyu bayan wani gwajin makami mai linzami da ta yi.

Wannan sabon gwajin makaman dai, na zuwa ne gabanin ziyarar da mataimakiyar shugabar Amirka Kamala Harris za ta kai makwabaciyar Koriya ta Arewan kana abokiyar tagwaitakarta da kuma takun sakarta Koriya ta Kudu. Rundunar sojojin Koriya ta Kudun ta bayyana cewa, ta gano makamai masu linzami da ba sa cin dogon zango guda biyu da aka harba daga fadar Pyongyang. Rahotanni sun nunar da cewa an harba makami na biyu, mintuna 10 bayan harba na farko. 

Categories
Siyasa

EU ta sake saka takunkumi akan Rasha da zai shafi Man da take fitarwa.

Majalisar gudanarwar Turai. AP – Jean-Francois Badias

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sake kakaba wasu kunshin takunkuman karya tattalin arziki kan Rasha dangane da abin da ta ke aikatawa a Ukraine, cikin takunkuman har da wanda ya kayyade farashin mai da kuma hana fitar da kayayyakin da Moscow ke yi na kusan yuro biliyan bakwai.

Shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen ta ce takunmuman sun kuma kunshi hana wasu da ke taimakawa Rasha tafiye-tafiye da kuma kama wasu kaddarorin su.

Kunshin takunkuman sun kuma haramtawa turawa zama mamba a kwamitocin gudanarwar kamfanoni mallakar gwamnatin Rasha.

Shima jami’in kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Josep Borrell, ya ce mutanen da wannan takunkumi ya shafa sun hada da wadanda ke taimakawa Moscow wajen kaucewa takunkumin da aka sanya mata.

Tun a watan Mayun da ya gabata, kungiyar ta EU ta amince da haramta shigar da mafi yawan man Rasha zuwa nahiyar.

Yunkurin kara farashin man da EU ta yi, na nufin kayyade yawan kudaden da kasashe irin su China da India ke biya na danyen man Rasha. Tushen wannan labari daga RFI Hausa.

Categories
Siyasa

Buhari ya a Mince da A siyawa NDLEA Mutoci masu Sulki.

Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe naira miliyan N580.5 don sayo motoci masu silke da zimmar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA).ke yi.

NDLEA na ƙarƙashin kulawar ofishin Ma’aikatar Shari’a wadda kuma ita ce ta gabatar da ƙudirin neman sayen motocin, kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na yau Laraba.

A cewarsa: “Daliln da ya sa aka gabatar da ƙudirin shi ne don a nemi amincewar majalisar wajen bayar da kwangilar sayo motoci huɗu masu silke da ke da kujeru 14 ga NDLEA.”

Ya ƙara da cewa an yanke shawarar sayo motocin ne da zimmar kare rayuwar jami’an hukumar ta NDLEA “da ke aiki tuƙuru don ba da sakamako mai kyau”.

Kuɗin sun ƙunshi kashi 7.5 cikin 100 na kuɗin harajin VAT na tsawon mako 16, a cewar ministan.

Categories
Siyasa

Buhari ya a Mince da A siyawa NDLEA Mutoci masu Sulki.

Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe naira miliyan N580.5 don sayo motoci masu silke da zimmar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA).ke yi.

NDLEA na ƙarƙashin kulawar ofishin Ma’aikatar Shari’a wadda kuma ita ce ta gabatar da ƙudirin neman sayen motocin, kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na yau Laraba.

A cewarsa: “Daliln da ya sa aka gabatar da ƙudirin shi ne don a nemi amincewar majalisar wajen bayar da kwangilar sayo motoci huɗu masu silke da ke da kujeru 14 ga NDLEA.”

Ya ƙara da cewa an yanke shawarar sayo motocin ne da zimmar kare rayuwar jami’an hukumar ta NDLEA “da ke aiki tuƙuru don ba da sakamako mai kyau”.

Kuɗin sun ƙunshi kashi 7.5 cikin 100 na kuɗin harajin VAT na tsawon mako 16, a cewar ministan.

Design a site like this with WordPress.com
Get started