Categories
Wasanni

Man City ta lallasa Man United da Kwallaye A. Gasar premier

Manchester City ta doke Manchester United da ci 6-3 a wasan makon na takwas a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Etihad.

Tun kan hutu City ta ci kwallo 4-0 ta hannun Phil Foden da Erling Haaland kowanne ya ci bibiyu.

Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu Foden da Haaland kowanne ya kara zura kwallo a raga.

Sai dai United ta zare uku ta hannun Dos Santos, sannan Anthony Martial ya zura biyu a raga daya daga ciki a bugun fenariti.

Da wannan sakamakon City tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 20, United kuwa tana nan da makinta 12 tana ta shida a teburin wasannin bana.

Manchester City ta yi nasara karo uku a jere a kan United tun bayan doke ta hudu da ta yi tsakanin Afirilun 2013 zuwa Nuwambar 2014.

United ta yi rashin nasara karo na 18 a Premier League a hannun City, – Liverpool da Chelsea sun yi nasara a kan United irin haka a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wasan da suka fafata a bara:

2021/2022

Premier League Lahadi 6 ga watan Maris 2022           

  • Man City         4 – 1     Man Utd         

Premier League 6 ga watan Nuwamba 2021         

  • Man Utd          0 – 2     Man City
Design a site like this with WordPress.com
Get started